Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Zafi ya hallaka mutane 800 a Pakistan

Mutane kimanin dari takwas ne suka hallaka a 'yan kwanakin nan, sakamakon cucuttukan da ke nasaba da matsanancin zafi a Kudancin Pakistan inda ake zafin da ya kai maki 45 a ma'aunin Celsius.

Tuni dai aka bayyana dokar ta baci a asibitoci a duk fadin lardin Sindh.

Birnin Karachi shi ne yankin da matsalar ta fi kamari.

Ga dai Isa Sanusi.