Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Hare-haren bam a Jos

A Najeriya, an yi jana'izar mutane 48 da aka kashe a hare-haren bam a birnin Jos na jihar Pilato.

Wasu karin mutanen kimanin saba'in da hudu kuma na jinya a asibiti. An kai hare-haren ne a wani gidan cin abinci da kuma wani masallaci.

Ana dai danganta irin wadannan hare-hare da kungiyar Boko Haram, wadda ta hallaka mutane da dama a jihar Borno a makon jiya.

Ga dai Jimeh Saleh da karin bayani: