Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Har yanzu al'ummar Gaza na cikin tasku

Shekara guda kenan tun bayan barkewar yaki tsakanin Isra'ila da Hamas a Gaza. A cewar majalisar dinkin duniya, Falasdinawa dubu biyu da dari biyu ne suka hallaka, tare da Isra'ilawa saba'in da uku. Kimanin mutane dubu dari kuma sun rasa muhallinsu a Gazar. Isra'ila da Masar sun tsaurara matakan tsaro a iyakokinsu da Falasdinu. To amma hakan ya janyo babban cikas wajen sake gine-gine. Ga rahoton Elhadji Diori Coulibaly