Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Yaya masu dafa abinci ke yi lokacin Azumi?

Azumin Ramadan dai, lokaci ne da Musulmi ke kokarin kama kansu da kuma kaucewa abubuwan da zuciyarsu ke sha'awa. Sai dai ko yaya batun yake ga Musulman da ke aiki a gidajen dafa abinci? A ci gaba da rahotannimu kan Azumin na Ramadan a sassa daban-daban na duniya, yau za mu leka Lebanon ne don zantawa da wani kuku, wanda ke shirya abincin buda baki ga mutane dari 3 a kowacce rana.