shirin raayi riga
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Bukukuwan Sallah da tsaro

A lokacin da al'ummar musulmi ke bukukuwan sallar azumi, matsalar tsaro na cigaba da zama kalubale a Najeriya da ma wasu kasashen da ke makwabtaka da ita.

Ana dai daukar matakai da dama da nufin dakile hare haren da ake zargi 'yan Boko Haram ke kaiwa, cikin matakan har da hana sa Nikabi a wasu kasashen da kuma nadin sabbin hafsoshin tsaro da shugaban Najeriya ya yi.

Shin ko yaya ku ke kallon wadannan matakan? kuma ta yaya matsalar tsaron ke shafar hidimar sallar a inda ku ke?

Wannan shine batun da za mu tattauna a filin ra'ayi riga na wannan makon.