habre
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Habre ya bayyana gaban kotu a Senegal

An soma wata muhimmiyar shari'a a Senegal, ta tsohon shugaban Chadi Hissene Habre, wanda ake zargi da aikata mugayen laifufuka a kan bil'adama. Da karfin tuwo aka kai Habren kotun, kafin daga baya jami'an tsaro su dauke shi nan da nan, sakamakon ja-in-ja tsakanin magoya bayansa da jami'ai. Wannan ne karon farko da wata kasar Afirka ta tuhumi tsohon shugaban wata kasa a nahiyar, tare da goyon bayan Tarayyar Afirka. Ga Ibrahim Isa da karin bayyani: