Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mani Hanya 25/07/2015

Najeriya ta cika shekara guda ba tare da samun wani ya sake kamuwa da cutar shan inna ba.

Hukumomin kasar sun ce sun dauki matakai da dama tare da hadin gwuiwar sauran masu aikin sa- kai, a kokarin da suka yi wajen kawar da cutar baki daya daga kasar.

Najeriyar dai ta gamu da matsaloli wajen yaki da cutar ta shan inna, irin su kyamar Allurar Rigakafi, da rashin kai wa ga yara dake kauyuka masu nisa, da kuma sanya addini da siyasa a batun na Poliyo.

Dr Ado Muhammad, shi ne shugaban hukumar kula da harkokin lafiya a matakin farko ta tarayya a Najeriya, kuma a filinmu na Gane Mini Hanya na wannan makon, ya yi wa Bashir Sa'ad Abdullahi karin bayani kan matsayin da ake ciki na yaki da cutar Polio a kasar.