An kirkiro na'ura mai gane fuska a duhu

Fuskar mutum Hakkin mallakar hoto SPL
Image caption Na'urar na iya gane fuskar mutum ta hanyar amfani da dumin jikinsa da kuma wani nau'in haske da ido ba ya gani

An kirkiro na'ura mai gane fuska a duhu

Masu binciken kimiyya a wata jami'a a jamus sun kirkiro na'urar mai iya gane fuska a cikin duhu.

Sabuwar na'urar mai wannan fasaha na amfani ne da dumin jikin mutum da kuma nau'in hasken 'infred' wanda ido ba ya gani da kuma hoto don gano surar mutum a duhu.

Dr. Saquib Sarfaz daya daga cikin wandan suka kirkiri fasahar yace ba su da niyar sa fasahar a kasuwa a yanzu.

Masu binciken kimiyyar Dr. Sarfaz da Dr. Rainer sun shaidawa BBC cewa sun dauki shekaru su na binciken fasahar yadda nu'urar za ta gane fuskan dan adam sakamakon sha'awarasu da gano yadda kimiyya ka iya maganin matsalar.