Za'a iya yaudarar na'urar bin diddigin motoci

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Na'urar bin diddigi motocin na hana satar motocin ta hanyar tauraraon dan adam

Wani mai bincike ya gano cewa za'a iya yaudarar na'urar gano inda motoci da bayanan karya.

Kamfanoni da dai-daikun jama'a na amfani da na'urar Goldstar mai aiki da tauraron dan adam don bin diddigin motoci ko kontaina ko jiragen ruwa yayin da suke zirzirga daga nan zuwa can a bisa bayanan da aka sa mata.

Amma Colby Moore, wani kwararre a fasahar tsaro ya gano cewa wannan na'urar na da matsalar hanyar tattara bayanai da kuma sarrafa shi wanda zai iya sa bata gari su sarrafa ta .

Za su iya yin hakan ne saboda hanyoyi aikawa da bayanai tsakanin yi na'urar da tauraron dan adam a bude suke, kuma bayanan da ake turawa na'ura ba ta iya tantance sahihancin wanda ya tura.

Kamfani Goldster dai bace komai ba game da wannan binciken