Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

An bukaci 'yan Burundi su kwantar da hankali

Shugaban Burundi, Pierre Nkurunziza, ya nemi a kwantar da hankali, bayan da a jiya wasu 'yan bindiga sanye da kayan soja, suka hallaka daya daga cikin na kurkusa da shi, a Bujumbura, babban birnin kasar. A cewar wani kakakin shugaban, neman yin ramuwar gayya ga kisan Janar Adolphe Nshimi-rimana, zai yi zagon kasa ga zaman lafiya a kasar. Ga rahoton Isa Sanusi: