Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

'Yan sanda sun harbi matashi a Ferguson na Amurka

'Yan sanda a Amirka sun tuhumi wani bakar fata dan shekara sha takwas, da harbinsu a lokacin wani taron gangami, jiya da dare. Yanzu haka Tyrone Harris din na can kwance a asibiti, rai ga hannun mai shi, bayan 'yan sandan sun mayar da martani. An gudanar da gangamin a garin Ferguson na jahar Missouri, don tunawa da mutuwar wani matashi bakar fata, Michael Brown, wanda wani dan sanda farar fata ya bindige har lahira, shekara guda kenan. An kafa dokar ta baci. Ga rahoton Isa Sanusi: