Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Mawakin kasar Togo, King Mensah

Bari kuma mu sadu da sarkin mawakan Togo - daya daga cikin mawakan da suka yi suna a Afirka ta yamma. A cikin shekaru ashirin na wake-waken nasa, King Mensah ya kade duniya. Galibi yana tabo batutuwan da suka shafi wadanda ke fama da kunci, da kuma matalauta a wakokin nasa. Don haka ne ma ya bude wani gidan marayu, don kare yara da kuma ilimantar da su. Ga dai labarin King Mensah din