Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Hira da Archbishop Idowu Fearon a kan Boko Haram

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya ba sabbin shugabannin sojojin kasar wa'adin watanni uku, na su murkushe 'yan Boko Haram. Sai dai wasu na ganin cewa, baya ga karfin soja, akwai bukatar a sauya tunanin 'yan Boko Haram din. Daga cikinsu har da sabon sakatare Janar din cocin Anglican, mai mabiya miliyan tamanin da biyar a duniya. Archbishop Josiah Idowu-Fearon ya bayyana hakan ne a hirar da muka yi dazu da shi. Amma ya soma ne da batun samun hadin kan addinai a Najeriyar: