CCTV ta nuna wanda ake zargi a Bangkok

Image caption Wanda ake zargin ya kai harin bam din a Bangkok

An gano wani faifan bidiyo daga na'urar CCTV wanda jami'an tsaro suka ce yana da nasaba da harin bam din da aka kai a Bangkok babban birnin kasar Thailand.

Jami'an tsaro na gudanar da bincike kan faifan bidiyon, amma dai abin da kyamarar CCTV din ta nuna mana mutumin ba dan kasar Thailand bane.

Firai ministan Thailand ya bayyana harin bam din da ya hallaka mutane a kalla ashirin a wani wurin ibadar Hindu a Bangkok a matsayin lamari mafi muni da ya faru a kasar.

Prayut Chan-o-Cha ya ce an hangi wani mutum wanda ake zargi a kamarar tsaro, ya shiga wurin ibadar dauke da wani kunshi ya kuma fita ba tare da kunshin ba.

Mai magana da yawun mukaddashin shugaban kasar Manjo Janar Weerachoon Sukhonta-patipak, ya ce suna kokarin su gano ko shi mutumin wanene, da kuma tabbatar da lallai yana da alaka da harin bam din.