Jirgi maras matuki na harzuka Tunku

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption jiragen marasa matuka ana sarrafasu daga nesa ne.

Jirgi maras matuki na harzuka Tunku

Wani bincike ya nuna cewa dabban dawa Tunku na kaduwa a yayin da jirage masu sarrafa kansu suka yi shawagi kusa da su.

Wasu masu gudanar da bincike daga jami'ar Minnesota sun makala wata na'ura mai auna lafiya a jikin wasu Tunku su 6 sannan suka auna bayanan da ta bayar a yayin shawagin jiragin sama marasa matuki sau 17.

Sakamakon ya nuna bugun zuciyar wadannan dabbobin dawa sun karu a lokacin da jiragen suka rika yin shawagi mita 20 kusa da inda suke.

Masu binciken sun ce da akwai bukatar aci gaba da bincke ta hanyar kara yawan shawagin ko watakila Tunkun za su saba da jiragen sakamakon tsawaitar lokaci.

Na'urori masu shawagi wadanda ake sarrafa su daga nesa na da matukar amfani ga masu bincike a harkar kula da namun daji saboda za'su iya lekawa loko da sakon daji, su kuma sa ido akan dabbobin dawa daga nesa.