Mai kutse a komfutoci 77,000 ya shiga hannu

computer Hakkin mallakar hoto
Image caption Masu kutse a computer na shigar burtu ne kamar yadda Coker yayi a shafukan mutane na dandalin sada zumunta da muhawara na Facebook

An cafke wani mazaunin New york mai amfani da sunan karya da yin kutse a cikin komfutoci sama da 77,000 na masu amfani da dandalin sada zumunta da takfa muhawara na Facebook.

Mutumin yayi amfani da shafukan da ya yi kutsen wajen aika wasiku ga abokan wadanda ya yiwa kutsen da zummar cewa mai shafin ne, ba tare da saninsu ba, da kuma ainihin mai shafin.

Eric Crocker na daya daga cikin mutane 70 da aka kama da aikata wannan laifi. A Amurka kadai an kama mutane 12 a cikin wani shiri na musamman na yaki da laifukan da suka shafi yanar gizo a duniya mai lakabi da 'Operation Shrouded Horizon'

An gurfanar da Croker a kotu a inda aka tuhume shi da karya dokar da ta hana aika wasikun zamba da kuma amfani da yanar gizo ta hanyar da ba ta kamata ba.

Croker shi da sauran masu kutse a dandalin Facebook suna samun dalar Amurka 300 akan komfutoci 10,000 da suka yiwa kutse.

Kotun za ta yanke mi shi hukunci ranar 23 ga watan Nuwamba mai zuwa Idan aka same shi da laifi za'a iya daure shi har na tsawon shekara 3 ko kuma ya biya tarar $250,000 ko kuma duk.