Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Dogayen benaye na birnin New York

Yanzu kuma bari mu leka birnin New York, inda ake gina wasu dogayen benaye na kasaita, wadanda sai wane da wane ne ke iya zama a cikinsu.

Yanzu haka dai ana sayer da wasu daga cikin irin wadannan gidaje a kan kusan dala miliyan 100 kowannensu.

Gibi tsakanin masu hannu da shuni da talakawa dai, batu ne da zai janyo muhawara a gabannin zaben shugaban kasa na badi. Ga dai Abdullahi Tanko Bala da karin bayani: