Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Iran ta ba BBC izinin shiga kasar a karon farko cikin shekaru 6

Shekaru shidda kenan da hukumomin Iran suka tesa keyar wakilin BBC na karshe a kasar. Yanzu hukumomin na Iran sun ba BBC izinin shafe mako guda a cikin kasar domin hada rahotanni. Iran dai na makwabtaka da kasashe masu fama da rikicin siyasa, kamar Iraki. To ko me hakan yake nufi ga rawar da kasar ke fatan takawa a Gabas Ta Tsakiya? Ga rahoton Aminu Abdulkadir.