Fallasa ba ta hana mutane shiga shafin Ashley Madison ba

Ashley Modison Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Masu satar bayanai sun yi kutse cikin shafin sun kuma kwarmata bayanan sirri na mutane a watan Agusta. Wand hakan ya sa daya sun ji kunya

Duk da kutsen da masu satar bayanai suka yi tare da bankadar sunayen ma'abota shafin zawarci da samartaka na Ashley Madison mutane ba su daina tururuwar yin rajista da shafin ba.

Dubun dubatar mutane ne suka yi rajistar shiga shafin na Ashley Madison a makon da ya wuce a cewar masu shafin Avid life Media.

Bayanan sama da mutane miliyan 33 ne aka sace daga shafin na intanet aka kuma kwarmata a watan Agusta.

Bayanan da aka kwarmata sun hada da cikkkakun sunaye da adireshin email da lambobin katin banki (credit card) ciki har da sakonnin email na shugaban kamfanin Mista Biderman.

A Juma'ar da ta gabata ne shugaban kamfanin ya ajiye mukaminsa wanda kamfanin ya ambata da cewa ya yi hakan ne domin kare mutuncinsa.