Google da Apple sun kulla dangantaka

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Agogon zamani na Android da iphone da ake kira da kuma amsa waya

Kamfanin Google ya mayar da manhajarsa ta Android wadda za a iya daurawa ta yi aiki da ta Kamfanin Apple a manhajar iOS.

Wannan ci gaba na nufin cewa masu agogon hannu na manhajar Android za su iya amfani da wayar salula ta iphone a karo na farko.

Hakan dai zai habaka kasuwar agogunan hannu na zamani kuma zai zama kalubale ga kamfanin nan Apple.

Wannan sabon ci gaba na nufin masu agogon hannun za su iya kiran waya ko su amsa kira.

Haka kuma za su iya duba sakonnin ka-ta-kwana na text, har ma da duba lafiyar zuciyarsu ta hanyar yadda ta ke bugawa.