Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mani Hanya 05/09/2015

A karshen makon nan ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya cika kwanaki 100 da rantsar da shi a matsayin shugaban kasa mai cikakken iko.

'Yan kasar da dama suna bayyana ra'ayoyi daban-daban dangane da salon tafiyar da mulkin shugaban kawo yanzu.

A lokacin da yake yakin neman zabe, abubuwa uku ne Muhammadu Buharin ya yi alkawarin zai fi mai da hankali a kai.

Abubuwan kuwa sun hada da batun tsaro, da yaki da cin hanci da kuma samar da ayyukan yi.

Wakilinmu a Kano Yusuf Ibrahim Yakasai, ya tattauna da Dr. Junaidu Muhammad, wani tsohon dan siyasa, kuma mai sharhi kan al'amuran yau da kullum kan yadda yake kallon kamun ludayin Shugaba Buharin kawo yanzu.