McAfee zai fito takarar shugabancin Amurka

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jonh McAfee wanda ya kirkiri mahajar maganin illolin komfuta ya kuma sa sunansa 1987

Mista John McAfee wanda ya kirkiro kamfanin manhajar da ke maganin illolin Komfuta watau Anti virus ya nuna aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin Amurka.

Dan kasuwa McAfee ya yi suna ne a 1987 a lokacin da ya kirkiro kamfanin manhajar maganin illolin komfutar sannan ya sanya wa kamfanin sunansa, ya kuma ajiye aiki a kamfanin a 1994.

Daga baya kamfanin Intel ya saye kamfanin shi kuwa masanin ilimin komfutar McAfee ya zama ba shi da sauran hannun jari a cikinsa.

Tuni dai McAfee ya kaddamar da shafin intanet na yakin neman zabe zai kuma fitar da karin bayani dangane da takarar ta sa a nan gaba.