Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Shirin sauya tunanin 'yan Boko Haram

Bayanai daga gidaje yari daban-daban a Najeriya sun nuna cewa hukumomi na can sun dukufa kan kokarin sauya tunani mayakan kungiyar Boko Haram da ake tsare da su a ciki, a zaman wata hanyar yakar ta'addanci da tsattsauran ra'ayi ta ruwan sanyi.

Ofishin mai bai wa shugaban kasar shawara kan tsaro ne ke gudanar da aikin na sauya tunani a karkashi wani sabon shiri na yaki da tsattsauran ra'ayi aka fi sani da CVE wato Countering Violent Extremism.

Cibiyar yaki da ta'addanci ta duniya wato Global Counter-terrorism Forum ke daukar nauyin gudanar da wannan shirin a kasashen da ke fuskantar barazanar ta'addanci a duniya.

Wata tawagar BBC ta samu kutsa kai cikin daya daga cikin gidajen yarin Najeriya da ake wannnan shirin ga kuma rahoton da Haruna Shehu Tangaza daya daga cikin 'yan tawagar ya shirya mana: