Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

A bana damuna ta kankama a wasu wurare

Hakkin mallakar hoto afp

Galibin manoma a Nahiyar Afirka, kudu da hamadar sahara sun dogara ne ga noman damina.

Daminar kan bambanta daga sashi zuwa sashi, wanda hakan kan yi tasiri ga irin yabanya ko kuma amfanin gonar da akan samu.

A bana dai, yayin da damunar ta kankama a wasu wuraren, a wasu yankunan kuwa har yanzu shukar ba ta kosa ba.