Yadda zaka samar da kalmar sirri mai inganci

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Kalmar sirri na tamakar makulli ce

Nasarar masu kutse da suka samu na warware sarkakiyar sama da kalmomin sirrin miliyan 11 da suka sato daga shafin samartaka da zawarci na Ashley Madison ya fito da muhimmancin tsaron kalmar sirri.

A ranar talata ne wata hukumar gwammnatin Ingila GCHQ ta wallafa wasu matakai da aka tsara domin su inganta tsaro su kuma inganta amfani da na'urori masu kwakwalwa.

Rahoton ya kalubalanci wadansu tunani na gama gari game da kalmomin sirri da kuma tsaro. Shin yaya zaka iya zabar kalmar sirri mai nagarta da kuma kuma iya tuna ta?

Shafukan intanet da yawa na bukatar kalmar sirri masu tsauri masu hade da manyan baki da kanana gami da lambobi da kuma alamu.

Rahoton GCHQ ya bayar da shawarar cewa kalmomin sirri masu tsauri na da nasu matsalolin saboda yawancin mutane na rubuta su ne su kuma yi amfani da su a shafuka da yawa a intanet.

A cewar Dr Steven Murdoch na sashen ilimin kimiyyar komfuta, 'ba lalle bane ya kasance cewa tsauraran kalmomin sirri na samar da kariya'.

'Sai dai' in ji shi, 'ci gaba da cewa komfutoci masu nagarta bai kamata su dogara da kalmar sirri guda ba, sai dai su samar da karin tsaro wanda za'a iya gano wata bakuwar dabi'a da zai sa kare mai amfani na'urar.