Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mani Hanya 12/09/2015

Bayanai daga gidajen yari daban-daban a Najeriya sun nuna cewa hukumomi na can sun dukufa kan kokarin sauya tunanin mayakan kungiyar Boko Haram da ake tsare da su a gidaje yari, a zaman wata hanyar yakar ta'addanci da tsattsauran ra'ayi ta ruwan sanyi.

Ofishin mai bai wa shugaban kasar shawara kan tsaro ne ke gudanar da aikin na sauya tunanin a karkashin wani sabon shiri na yaki da tsattsauran ra'ayi da aka fi sani da CVE wato Countering Violent Extremism.

Cibiyar yaki da ta'addanci ta duniya wato Global Counter-terrorism Forum ke daukar nauyin gudanar da wannan shirin a kasashen da ke fuskantar barazanar ta'addanci a duniya.

Wata tawagar BBC ta samu kutsa kai cikin daya daga cikin gidajen yarin Najeriya da ake wannnan shirin ga kuma rahoton da Haruna Shehu Tangaza daya daga cikin 'yan tawagar, ya shirya mana.