BBC ta jinkirta raba wa yara komfutoci

Image caption komfuta da yara

An jinkirta shirin BBC na raba kananan komfutoci miliyan daya ga yara 'yan makaranta a watan Oktoba .

Matsalar wutar lantaki da na'urorin suka samu za ta sa sai bayan Kirsimeti za a raba kwafutocin, in ji wani kakakin hukumar BBC.

An kirkiri 'yar karamar Komfutar ce domin sa wa yara sha'awar yadda ake kirkirar manhaja.

A cewar sa, matsalar da ta janyo jinkirin raba kwafutocin ta shafi yawancin kananan kwamfutocin da ake son rarraba wa, yana mai cewa burin BBC shi ne a samu kwamfutoci masu inganci.

Ana sa ran rarraba kananan kwamfutocin ne ga 'yan shekara 11 zuwa 12.