Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

An kaddamar da jirgin kasa na zamani a Ethiopia

Ethiopia ta kaddamar da jirgin kasa mai aiki da wutar lantarki, wanda zai rika zurga-zurga a Addis Ababa, babban birnin kasar.

Shirin wanda ya ci zunzuruntu kudi dala miliyan dari hudu da saba'in, shi ne irinsa na farko a kasashen Afrika Kudu da Hamadar Sahara.

Daruruwan jamaa ne cikin annashuwa, suka halarcin birkin kaddamarwar. Ga dai rahoton Aichatou Moussa.