Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Kasuwar raguna ta yi kasa a Nigeria

Rahotanni daga kasuwannin raguna daban-daban a Najeriya na nuna cewa farashin dabbobi musamman raguna ya sauka kasa a daidai lokacin miliyoyin musulmi ke shirin shagulgulan babbar sallah a gobe. Wasu da BBC ta tuntuba a jihohi kamar Kano da Sakkwato da Zamfara da kuma birnin a Abuja sun ce farashin dabobin ya suka ne sakamakon rashin kudi a hannu jama'a. Ana dai bukatar kowane musulmi da ke da hali ya yanka rago,ko saniya ko rakumi ko ma Akuya akalla daya a lokacin wannan bukin wanda shi ne mafi girma a addinin musulunci. Halima Umar Saleh ta tattauna da wasu masu sayar da dabbobi a Kano.