Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Hadarin da ya auku a Saudiyya

A ranar Alhamis ne mutane sama da dari bakwai suka rasa rayukansu , sakamakon wani turmutsitsi a hanyar zuwa jifan shaidan yayin aikin hajjin bana a Saudiyya. Wannan dai ba shi ne karon farko da irin haka ke faruwa ba. Shin mene ne ya faru, kuma wadanne hanyoyi za a bi a kauce ma irin wannan hadari? Laifin na tsare tsare ne ko kuwa na na mahajjata? Wasu kenan daga cikin abubuwan da zamu tattauna a filinmu na Ra'ayi Riga.