Zuckerberg zai sa Intanet a sansanonin 'yan gudun hijira

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Mark Zuckerberg wanda ya kirkiro dandalin muhawara da sada zumunta Facebook kuma shugaban kamfanin

Wanda ya kirkiro dandalin muhawara da sada zumunta na Face Book ya sanar da cewa zai taimaka wajen samar da intanet a sansanonin 'yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya.

A yayin da yake jawabi a wani taro a New York Mista Zuckerberg ya ce hakan zai taimakawa 'yan gudun hijirar samun taimako da kuma ci gaba da sada zumanta da iyalansu.

Ya kuma kara da cewa Face Book zai shiga cikin wani tsarin gangami na samar da intanet din ga kowa da kowa a duniya nan da shekaru 5.

Shugaban na Face Book ya ce hanyar sadarwa ta intanet za ta taimakawa Majalisar Dinkin duniyar cimma muradan ci gaba wadanda za su fitar da jama a daga kangin fatara.

Kimanin mutane biliyan 3 ne a duniya ke da intanet, shirin na aniyar samar da intanet ne ga karin mutane bilyan 4 wadanda ba su da shi.

Zuckerberg ya ce yawan masu amfani da dandalin muhawara da sada zumunta na Face Book ya kai biliyan 1 da miliyan 5 a wata guda.

Haka nan kuma a karon farko dandalin na Face Book ya samu adadin mutane biliyan 1 masu amfani da shi a rana.

Kamfanin Face Book zai yi aiki ne tare da shugaban hukumar kula da 'yan gudun Hijira ta majalisar dinkin Duniya.

Ya kuma yi hasashen cewa yawan masu amfani da dandalin zai ci gaba da karuwa.