buhari
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Sunayen ministocin Nigeria

A ranar talata ne ake sa ran majalisar dattawa ta Najeriya za ta soma tantance kashin farko na sunayen mutane 21 da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika mata a matsayin wadanda yake son nadawa Ministoci.

Tuni dai Shugaban majalisar a cikin makon nan ya bayyana sunayen mutanen.

Yanzu haka kuma rahotanni na nuna cewar wadannan mutane na kokarin cika sharuddan bayyana a gaban majalisar domin tantancewa.To ko yaya kuke kallon wannan mataki?