Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Kallabi tsakanin rawwuna a Afrika ta Kudu

Bari mu gabatar maku da wani sabon babi da zu kawo a kakar farko, mai taken 'Matan Afrika' wanda zai hasko matan da suka yi fice a nahiyar Afrika gabaki daya, kuma za mu gabatar ne cikin makonnin da ke tafe.

Babi na farko zai gabatar da gwarzayen Afrika su takwas da ba a san da su ba, wadanda suka inganta rayuwar al'ummar cikin kasashensu, da kuma na waje.

Wacce za mu gabatar a farkon wannan babi ita ce Phindile Sithole-Spong, 'yar asalin Afrika ta Kudu ce mai dauke da cutar AIDS/HIV watau 'kanjamau, kuma ta dukufa da yakin nema wa masu cutar 'yanci daga wariya da kyamar al'umma da kuma samun ingantacciyar lafiya, musamman tsakanin matasa.