Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ya Musulmi da Yahudawa ke kallon masallacin Kudus?

'Yan sandan Isra'ila sun harbe wasu Falasdinawa 2 a birnin Kudis. Shi ne tashin hankali na baya-bayan nan, yayinda ake samun karuwar hare-haren da Palasdinawa ke kaiwa da bindiga da kuma wukake, abun da ya janyo zaman dar-dar a yankin.

An yi arangama a Gabar Yammacin Kogin Jordan, kamar nan a Bethlehem. Tun farko Isra'ila ta tura karin sojoji zuwa yankunan da aka fi hare-hare da kuma wasu bangarori na birnin Kudis.

To rikicin dai ya fara ne a farkon watan Oktoba inda aka yi artabu a massalacin Al Aqsa. To ko mene ne dalili? Ga dai rahoton Muhammad Kabir Muhammad.