Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Hira da gwamna Bindow Jibrilla na Adamawa

Gwamnan jihar Adamawa a arewa maso gabashin Najeriya ya ce yawan 'yan gudun hijirar da ke kwarara zuwa cikin jihar na son fin karfin gwamnatinsa.

Muhammad Bindow Jibrilla ya ce ko baya ga wadanda ke shiga jihar daga makwabatan jihohin Borno da Yobe masu fama da rikicin Boko Haram, yanzu jihar na karbar 'yan gudun hijara da ke gujewa fadace-fadace a Kamaru da Jamhuriyyar Tsakiyar Afrika.

A kan haka ya yi kira ga gwamnatoci da kuma kungiyoyi da sauran jama'a da su kawo wa jiharsa dauki domin taimaka mata wajen kula da dubun dubatar 'yan gudun hijirar.

Ga hirarsa da abokin aikinmu, Haruna Shehu Tangaza