Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Shugaba Xi Jinping na ziyara a London

An yi wa shugaban China, Xi Jinping liyafar ban girma a fadar Sarauniya ta Buckingham, yayin da ya fara ziyarar kwanaki hudu a Birtaniyar. Bangarorin biyu zasu kulla sabbin yarjajeniyoyin kasuwanci na biliyoyin daloli a lokacin ziyarar, kuma Burtaniya na fatan zama babbar kawar China a Turai. To sai dai masu kare hakkin bil'adama sun yi zanga zanga. Ga rahoton Alhaji Diori Coulibaly, a kan ranar farkon ta ziyarar Xi Jinping: