Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

'A Cire Tallafin Mai' - in ji Sarkin Kano

Sarkin Muhammadu Sanusi II ya jaddada bukatar gwamnati ta cire tallafin man petur baki ɗaya, sannan kuma ya shawarci gwamnatin tarayya da kuma fadar shugaban ƙasa su sake duba matsayinsu dangane da rage darajar naira.

(Ga rahoton da Isa Sanusi ya hada mana.)

Karanta cikkaken rahoton:

Sarkin Muhammadu Sanusi II ya jaddada bukatar gwamnati ta cire tallafin man fetur baki daya, sannan kuma ya shawarci gwamnatin tarayya da kuma fadar shugaban kasa su sake duba matsayinsu dangane da rage darajar kudin kasar watau naira.

Sarkin ya fadi hakan ne yayin wani taro a Lagos, inda ya ce, babu wata dabara a ci gaba da bayar da tallafi a farashin albarkatun man fetur.

Hakkin mallakar hoto AFP

Sarkin ya ce: "Dole ne a cire tallafin mai, kuma a kara yawan harajin da ake biya akan kayan da mutane suke saye yau da kullum VAT. Ba abu ne mai dorewa ba mu ci gaba da tattalin arzikin da ya dogara ga haraji daga cinikin mai, da kuma haraji daga kamfanonin wayar salula. Kamata yayia a duba wadannan batutuwa."

'Tsage Gaskiya'

Sarki Sanusi na biyu ya kara da cewa yana goyon bayan wannan gwamnati kuma yana son ganin wannan gwamnatin ta samu nasara, amma ya ce, zai fadi gaskiya, ba kawai abin da gwamnati za ta so ji ba ne.

Sarkin Kanon wanda ya taba rike mukamin gwamnan babban bankin Najeriya ya ce tsarin musayar naira da dalar Amurka da ake amfani da shi yanzu ba abu ne da zai dore ba.

Amma tuni aka ambato wani babban jami'i a babban bankin Najeriya yana mai da martani ga matsayin Sarkin Kano, yana mai cewa, ba zasu rage darajar naira ba.

Cikin watan jiya dai yayi wata ziyara a Faransa an ambato shugaba Muhammadu Buhari yana cewa, ba goyi bayan rage darajar naira ba.