Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Girgizar kasa ta hallaka mutane a Pakistan da Afghanistan

Mutane sama da 300 sun hallaka yau, a mummunar girgizar kasar da aka yi a arewa maso gabacin Afghanistan, da kuma a Pakistan. An kuma ji girgizar a arewacin Indiya da kasar Tajikistan. Wasu mata 'yan makaranta akalla sha biyu na daga cikin mamatan. Praministan Pakistan Nawaz Sharif, zai katse ziyarar da yake a kasashen waje don komawa gida. Ga dai rahoton Isa Sanusi