Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Matsalar 'yan ci rani a Turai

A kokarin da su ke na tinkarar matsalar tudadar 'yan ci-rani, shugabannin Turai sun amince su samar da karin wurare dubu dari a cibiyoyin karbar 'yan gudun hijirar, bayan wani taron gaggawa a Brussels. Nan da karshen shekara kasar Girka zata tallafa wa 'yan ci-rani dubu hamsin da taimakon majalisar dinkin duniya. Za a kuma samar da wasu gurabun dubu hamsin a kasashen Balkans. Ga rahoton Alhaji Diori Coulibaly: