Nigeria Rugby
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ko kun san cewa ana wasan zari-ruga a Nigeria?

To ranar Asabar ne za a yi wasan karshe na gasar cin kofin duniya na kwallon zari-ruga a Biritaniya tsakanin New Zealand da Australia. Amma ko kun san cewa a Najeriya ma ana wasan na kwallon zari-ruga? Hakika, farin jinin wasan ya ragu a Najeriyar, amma yanzu wasu tsaffin 'yan wasa a kasar na kokarin dawo da shi. Ga dai rahoton Abdullahi Kaura Abubakar.