Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Me ya janyo faduwar jirgin Rasha a Sinai ?

Kamfanin jiragen saman Rasha, wanda jirginsa ya fado a Masar a ranar Asabar, ya ce wani abu ne daga wajen jirgi zai iya haddasa hadarin. Ya ce jirgin ba shi da matsala kuma ba laifin matukinsa ba ne. Amma gwamnatin Rasha ta gargadi masu saurin yanke hukunci. Jirgin ya fado ne mintuna ashirin da uku bayan tashinsa daga wurin shakatawar Sharm El-Sheikh. A yau an kai gawarwakin farko zuwa birnin St Petersburg na Rasha. Ga rahoton Jimeh Saleh: