Esther Kalenzi
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Kashi na hudu na gwarzayen matan Afrika

Ga kashi na hudu na irin rahotannin da mu ke kawo maku, na gwarzayen matan Afirka da ba sanannu ba sosai. A yau Esther Kalenzi ce, mai shekaru ashirin da takwas, wadda ta kafa wata kungiya mai zaman kanta a Uganda, mai suna '40 Days Over 40 Smiles'. Ko 40-40 a takaice. Ta tara kusan dala dubu sittin ta hanyar Facebook da Twitter, a cikin shekaru uku. An yi amfani da kudaden wajen gina makwancin dalibai da kuma wuraren wasa ... Ga waka a bakin mai ita!