senegal
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Matsalar kwararowar hamada a Senegal

Ba matsalolin siyasa da na tattalin arziki ne kawai ke tilasta wa jama'a barin Afirka ba. Akwai kuma sauyin yanayi.

Majalisar dinkin duniya ta yi gargadin cewa, a shekaru biyar masu zuwa, mutane miliyan sittin zasu iya barin muhallinsu a yankin Afirka na kudu da hamadar Sahara, saboda yanayi marar kyau.

A wannan rahoton na Abdullahi Tanko Bala, za ku ga rawar da yanayi ke takawa wajen kaurar jama'a a yankin Louga na Senegal: