Wasu mata a birnin Abuja Najeriya
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi riga:Gudunmawar mata ga zaman lafiya

Mata a matsayin su na iyaye wadanda kuma ke kula da gida suna taka muhimmiyar rawa wajen wanzar da zaman lafiya mai dorewa a tsakanin al'umma sakamakon baiwar da Allah ya yi musu ta tausayi da hakuri da kuma dabarun sasanta tsakanin jama'a.

Watakila wannan ne yasa Majalisar Dinkin Duniya ta jaddada muhimmancin shigar da mata cikin duk wata hidima ta wanzar da zaman lafiya a tsakanin al'umma.