Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Za mu murkushe barayin shanu - Masari

Gwamnan jihar Katsina da ke arewacin Nigeria, Aminu Bello Masari ya sha alwashin kawo karshen barashin shanu da suka addabi jihar. A hirarsa da abokin aikinmu, Aliyu Abdullahi Tanko a lokacin da ya kawo mana ziyara a ofishinmu na London, Gwamna Masari ya ce suna hada kai da makwabtan jihohi domin magance matsalar. Amma ya soma ne da batun korafin da wasu jihohi suka yi kan batun biyan albashin ma'aikata.