Kutsen Kamfanin Vtech ya shafi mutane miliyan 5

Kutsen Kamfanin Vtech ya shafi mutane miliyan 5

Kamfanin sayar da kayan wasan yara masu ilimantarwa Vtech ya tabbatar da cewa kimanin abokan cinikinsa miliyan biyar ne satar bayanan da aka yiwa kamfani ranar juma'a ta shafa.

Abokan cinikin daga ko'ina ne a duniya ciki har da Amurka da Faransa da kuma China.

Kamfanin Vtech ya kuma dakatar da shafuknasa na intanet 13 bayan da aka yi kutse a cikin rumbum ajiye bayanansa na manhajar koyarwa ta Lodge.

Rumbun bayanan da aka yi kutsen na dauke da bayanan abokan cinikin kamfanin ciki har da bayannai akan kananan yara.

Babu bayanai game da katin biyan kudi sai dai Kamfanin Vtech din ya ce ya adana sunaye da addireshin aika sako na email da kalmar sirri, da tambayara sirri da kuma amsarta na gano kalmar sirrin.

Tarin bayanan sun hada da addireshin komputa, da adireshin gida na aika wasika da kuma bayanan sauko da manhajar abokan cinikin.

"Kutsen da aka yi wa Vtech ya nuna irin kalubalen da muke fuskanta a yau" a cewar Tod Beardsley manajar injiniyar a kamfanin Rapid 7 mai kula da tsaron intanet.

Sannan ya kara da cewa "Yana da matukar wahala zama mai kera kayan wasan yara da kuma babban kamfanin fasaha mai ingantaccen tsaro".

Farfesa Alan Wodward kwarerre akan samar da tsaro a intanet a jami'ar Surrey ya ce da dukkanin alamu kamfanin na Hong Kong ya fada hannun masu kutse ta hanyar fasaha mai sauki ta SQL.

"Wadannan kutsen sun zama annoba, ya kamata a dakatar da su. Ko da hakan na nufin tilastawa wadannan kamfanoni ta hanyar dora musu haraji mai yawa. Ya kamata a mayar da hankali a kuma sa ido kan wadanda aka dorawa alhakkin hakan"