Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Tanbihin rayuwar Oscar Pistorious

An samu zakaran tseren nan Oscar Pistorious da laifin aikata kisa bayan kotun koli ta Afrika ta kudu ta sauya hukuncin farko da wata kotu ta yanke masa na aikata kisa ba da gangan ba.

Ya kashe budurwarsa Reeva Stenkamp a watan Fabrairun 2013 bayan ya harbeta sau hudu ta kofar ban daki.

Yanzu dai ana yi masa daurin-talala ne bayan ya kwashe shekara daya a cikin daurin da aka yi masa na shekara biyar.

Pistorius zai koma kotu domin a sake yanke masa wani hukuncin.

BBC Hausa ta yi duba kan muhimman abubuwa kan rayuwar dan tseren.