syria
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Taron kan syria a Saudiyya

Kungiyoyin 'yan hamayya na Syria da ke yaki da shugaba Basharul Assaad na yin taro a Saudiyya domin ganin yadda za su hada kai a kan tattaunawa da ake sa ran farawa a farkon watan gobe na Janairu a kan Syriyar.

Tattaunawar, wadda ake yi a Riyadh, ita ce ta farko tun da aka fara rikicin Syria a shekaru hudu da rabi da su ka wuce.

Sulaiman Ibrahim Katsina ya tuntubi Muhammad Kaddam Siddiq Isa, mai sharhi a kan Gabas ta Tsakiya da ke zaune a Dubai, don jin dalilin da ya sa ba a tuntunbi kungiyoyin 'yan tawaye na Isis da Al Nusra ba a wannan taro.