Yahya Jammeh, shugaban Gambia
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

'Gambia kasar musulunci ce'

Shugaban Gambia Yahya Jammeh ya bayyana kasar a matsayin kasar musulunci.

Ya ce, hakan wani mataki ne da ya dace da ra'ayin musulmi masu rinjaye a kasar, kuma ya ce, wannan zai fitar da kasar daga tasirin mulkin mallaka.

Amma ya ce, za a kiyaye hakkokin dukkan 'yan kasar.

Shugaba Jammeh dai ya yi kaurin suna wajen yin irin wadannan ikirari cikin shekaru ashirin da daya da ya shafe yana mulkin kasar.

A shekara ta 2013 ya fitar da Gambia daga kungiyar Commonwealth, yana mai cewa, kungiya ce ta masu goyon bayan mulkin mallaka.

A shekara ta 2007 ya yi ikirarin cewa, ya gano maganin da zai warkar da cutar AIDS mai karya garkuwar jiki.