An umarci a yi wa jirage marasa matuki rajista

Daga yanzu jirage masu sarrafa kansu da kuma wadanda suka mallake su dole ne su yi rajista a Amurka daga 21 na wannan watan Disamba.

Duk wani jirgi mai sarrafa kansa da aka saya daga wannan rana dole ne a yi masa rajista kafin tashinsa na farko, a cewar hukumar kula da sufurin jiragen sama ta kasar.

An ba masu jiragen nan da watan Fabarairu na 2016 da su yi rajista, a inda aka yafe musu dala 5 domin su yi azama a cikin kwanaki 30.

Kakakin hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Amurka Les Dorr ya shaidawa BBC cewa, hukumar za ta yi kokarin ilimantar da wadanda ba su yi rajistar ba a maimakon hukunta su.

Ya kuma kara da cewa wadanda kuma suka ki su yi rajistan, "mu na da hanyoyin da za mu tilasta musu yin hakan".

Hukuncin da za'a yi musu zai kai tarar kimanin dala 27,500 amma a tsauraran mataki na hukunci, tarar laifin na iya kai kimanin dala 250,00 da kuma daurin shekara 3 a gidan yari.

Wadanda suka mallaki jiragen maras matukin da su ka wuce shekara 13 dole ne su yi rajista da kansu, wadanda ba su kai wannan shekaru ba kuwa, iyayensu ne za su yi rajistar a madadinsu.

Kowanne jirgi maras matukin za'a ba shi lamba ta daban wanda a za'a lika a jikin jirgin, a cewar hukumar.